Thursday, August 23, 2007

Maryam Hiyana & Suleiman Bobo

Assalamu Alaikum!
Hakika Suleiman (Bobo) da Maryam Hiyana sunyi kurkure ba karami ba, koda ma a wanne addini ne. Amma mu sauran musulman duniya abin da yakamata da mu shine; Kamar yadda yake a musulunce yadda d akaddara rabin imani ne. Wannan abu Allah ya riga da ya kaddara sai fara babu wani dan Adam ko Aljani da ya isa ya kawar da shi, dole sai ya faru. Hakika sunyi kuskure matuka ("Allah ya gafarta musu"). Jama'a ina so ku sani fa, babu wani wadda ya fi karfi wanna abu ya faru shi. Amma tunda sunyi nadama, shikenan in har sauran musulmai na duniya da hakki a kan wannan abu da ya faru. Dan Allah a gafarta musu kamar yadda Shi Suleiman din ya bukaci Musulman duniya da su yafe masa. Kuma ku sani cewa, Allah ubangiji yana yafewa wadda ya yafewa dan uwansa. Saboda yada wannan hoto na bidiyon Hiyana ba zai haifar maka da komai ba Illa raga darajar musulunci da al'adar Hausawa a idon duniya.